News
Fasinjojin Sun Tsallake Rijiya Da Baya, Bayan Jirgin Saman Da Suka Hau Ya Shige Cikin Jeji Da Su A Legas.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fasinjojin sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin saman da suka hau ya shige cikin jeji da su a Jihar Legas.
A yayin da ake ruwan sama ne wani jirgin fasinja jirgin mallakin kamfanin Dana Air ya zame daga kan titinsa a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas, sannan ya ci kasa a cikin jeji.
Mutum 10 Sun Mutu A Lokacin Da Wasu Jirage Masu Saukar Ungulu Su Kayi Karo Da Juna
Hakan ya sa fasinjojin ficewa cikin gaggawa don tsira da rayuwarsu da kuma guje wa abin da ke iya biyowa baya.
Bidiyon abin da ya faru da fasinjojin suka ɗauka bayan sun tsallake rijiya da baya ya nuna tayar gaban jirgin ta nuntse a kasa a cikin ciyayi.
Zuwa lokacin hada wannan labari dai hukumomi ko kamfanin Dana Air ba su ce komai kan lamarin ba.
Haka zalika babu bayanin ko wani ya samu rauni ko kuma asarar rai ba.
Aminiya
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
