Connect with us

News

Hukumar EFCC Na Tuhumar Emefiele Da Bada Kwangilar Buga Kudi Akan Sama Da Naira Bilyan 18

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta sake kai karar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefeile kara a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja.

Advertisement

A sabuwar tuhumar, Hukumar na zargin Emefiele da amincewa a buga takarduna kudi na milyan 684 da dubu 590 akan kudi naira bilyan 18 da milyan 96.

Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban Hukumar EFCC

Hukumar ta EFCC ta zargi tsohon gwamnan da karya doka domin cutar da jama’ar kasa a yayin aiwatar da shirinsa na canjin kudi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Advertisement

 

Hukumar ta zargi Emefiele da cire tsabar kudi naira bilyan 124 da milyan 800 daga cikin asusun tattara haraji na kasa.

Advertisement

Babban mai gabatar da kara na hukumar EFCC, Lauya Rotimi Oyedepo SAN, ya ce za’a gurfanar da Emefiele gaban mai shari’a Hamza Mu’azu kan sabbin tuhume-tuhume guda hudu, wanda suka shafi rashin yin biyayya ga doka, da buga kudi ta haramtacciyar hanya da sauran lefuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending