Connect with us

News

Hukumar EFCC ta haramtawa ofisoshin jakadanci hada-hada da Dalar Amurka

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta umarci dukkan ofisoshin jakadanci na Najerika su koma amfani da takardun Naira wajen dukkan hada-hadarsu ta kudi.

Advertisement

Kazalika, EFCC ta haramtawa ofisoshin jakadanci na kasashen ketare dake Najeria amfani da Dalar Amurka wajen hada-hadar kudi a cikin Najeriya.

Ƙaƙaniƙayin Bashi Ya Sa Matashi Basajar Sake Shiga Musulunci

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da hukumar EFCC ta aikewa ministan harkokin kasashen ketare, Ambasada Yusuf Tuggar, a ranar 5 ga watan Afrilu

Advertisement

Har ila yau, EFCC ta umarci ofisoshin jakadancin Najeriya Dake kasashen ketare su koma hada-hadar kudade da Nairar Najeriya.

A cewar EFCC, sabuwar dokar zata dakile tare da rage dogaro da Dalar Amurka a harkokin da suka shafi tattalin arzikin Najeriya.

Advertisement

Wasikar, mai dauke da sa hannun shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ta bayyana cewa aiwatar da wannan sabon tsari zai farfado da darajar Naira tare da daga darajarta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending