News
Ranar Tarin Fuka: Gwamnan Jihar Kano ta kammala shirye-shirye don gudanar da gwaji da kuma bayar da magani kyauta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shirye don gudanar da gwaji da kuma bayar da maganin cutar tarin fuka kyauta a jihar Kano na aƙalla yara 6,000
Kwamishinan Lafiyar Jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya baiyyana hakan ranar Litinin a Kano, hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunawa da ranar yaki da cutar tarin fuka ta duniya.
Kotuna guda biyu sun ba da umarni daban-daban kan korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu
Kamar yadda aka saba duk shekara, ranar 25 ga watan Maris, ita ce ranar da duniya ke tunawa da kuma sabunta yaki da cutar mai hadarin gaske.
Dr Labaran ya ce gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta kammala shirye-shirye don gudanar da gwaji da kuma bayar da maganin cutar tarin fuka kyauta a jihar Kano.
Ya yi kira ga duk mazauna jihar da su kai kansu a duba su idan suna fama da tari har na tsawon makonni biyu ko fiye, inda ya ce gwamnatin jihar ta samar da wani shiri na yi mazauna jihar gwaji da bayar da magungunan cutar kyauta.
Haka zakika Dr Labaran wanda ya yaba da kokarin da kungiyoyi masu bayar da tallafi ke yi wajen yaki da cutar tarin fuka da sauran cututtuka a jihar.
Dr Labaran ya ce a shekarar 2023, jihar ta samu akalla mutum 114 da aka gano aka yi musu magani a jihar Kano kuma babu wani yaro da ya mutu sakamakon cutar tarin fuka.
Kazalika, ya jaddada kudirin ma’aikatar na hada hannu da hukumomi masu bayar da tallafi don kawo karshen cutar tarin fuka a jihar.
