News
Aminu Ado Bayero Ba Zai Jagoranci Sallar Juma’a A Babban Masallacin Juma’a Na Cikin Gari —Rundunar ‘Yan Sanda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ba zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Kano ba kamar yadda ake ta yadawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usaini Gumel wanda ya bayyana hakan, yana mai cewa Aminu Ado Bayero zai yi Sallar Juma’a a masallacin da ke cikin fadar Nasarawa, inda yake zaune a halin yanzu.
Ainihin Abin Da Aka Tattauna A Ganawar Sirrin Tsakanin Gwamna Abba Da Nuhu Ribadu
Gumel ya kara da cewa ana sa ran shi kuma Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II zai jagoranci sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na cikin gari.
Jaridar Inda Ranka ta ga sanawar da hadiman Sarki Aminu Ado Bayero suka rika sanya wa tun a jiya cewa suna gayyatar masoya sarki da su fito domin raka shi zuwa sallah Juma’a a masallacin cikin garin kano.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai Na Najeriya NAN ta wayar tarho a ranar Juma’a cewa sarki Aminu ba zai gudanar da sallar Juma’a a masallacin cikin garin ba.
Ya kara da cewa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar za su samar da ingantaccen tsaro don baiwa mazauna birnin Kano damar gudanar da sallar jam’i cikin lumana.
“’Yan sanda za su ci gaba da samar da tsaro da ya dace domin tabbatar da hakan zai baiwa mazauna yankin damar gudanar da Sallar Juma’a cikin kwanciyar hankali ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyin su ba,” inji shi.
