News
Kamfanin wutar lantarki zai katsewa hedikwatar ‘yan Sanda da barikin sojoji wuta saboda bashi
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja ya bayyana sunayen wasu manyan ma’aikatun Gwamnati 25 da ba su biyan kudin wutar lantarki.
Kamfanin samar da wutar lantarkin ya bayyana haka na wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar cewa, za ta yankewa dukkanin abokan huldarsu da wasu manyan Ma’aikatun Gwamnati, da ba su biya bashi ba nan da zuwa ranar 3 ga watan Yuni.
Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League), karo na 15 a tarihinta.
Daga cikin ma’aikatun sun haɗa da hukumar rundunar Sojojin Najeriya ta sama, da ta kasa, da Gwamnatin Jihar Kogi da Gwamnatin Jihar Neja, da Ma’aikatar Ilimi da dai sauransu.
Sanarwar ta ce “su na sanar da kowa da kowa cewa Kamfanin samar da wutar lantarkin zai katse wuta ga wandanda ake bi bashin kudin wuta zuwa nan da ranar 3 ga Yunin 2024.”
Da yake jaddada mahimmancin biyan kuɗi akan lokaci don ci gaba da aikinsu, kamfanin ya ce “Biyan kuɗin wutar lantarki akan lokaci yana da mahimmanci don ci gaba da gudanar da aikinsu, da haɓaka abubuwan more rayuwa don tabbatar da samar da ingantacciyar lantarki mai inganci ga al’ummarmu.”
Channels TV
