Connect with us

News

Ƙungiyoyin ƙwadago  sun dakatar da yajin aiki na kwanaki 5

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon suka bayar da tabbacin janye yajin aikin.

A cewar Vanguard yayin tattaunawar ƙungiyoyin ƙwadagon da wakilcin gwamnatin Najeriyar na safiyar yau ne aka kai ga nasarar janye yajin aikin da misalin ƙarfe 10 na safiya wanda tuni ya kassara harkokin hada-hada a sassan ƙasar.

Sojoji Sun Lalata Sansanin ‘Yan Ta’adda A Jihohin Kaduna Da Katsina

Bayan tattaunawar, bayanai sun ce gwamnatin Najeriyar ta amince ta biya fiye da Naira dubu 60 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata, ko da ya ke za a shafe kwanaki 5 ana tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.

Buƙatar ƙarin albashin na da nasaba da matsin rayuwa da kuma hauhawar farashin kayaki da ake gani a ƙasar lamarin da ya jefa masu ƙaramin ƙarfi a ƙaƙa-nikayi.

Tsadar rayuwa ta kai ƙololuwa a ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar Afrika yayinda darajar kuɗin ƙasar ke ci gaba da sauka wanda ke da nasaba da yadda gwamnati ta karya darajar da kanta a lokuta daban-daban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending