News
Sojoji Sun Lalata Sansanin ‘Yan Ta’adda A Jihohin Kaduna Da Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jiragen yakin saman Operation Whirl Punch da Operation Hadarin Daji sun lalata sansanin ‘yan ta’adda a Jihohin Kaduna da Katsina.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Air Vice Marshal Edward Gakwet, cikin wata sanarwa, ya ce an kashe ‘yan ta’adda da dama a hare-haren jirgin yaki ta sama da suka kai.
A cewar AVM Gabkwet, ya ce dakarun sun kai hare-hare ta sama a Buharinyadi, da ke yankin dajin Bula a karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna tsakanin 30 zuwa 31 watan Mayu, 2024.
Leadership ta ruwaito cewa binciken da suka yi sun gano ‘yan ta’adda dauke da makamai da ke yawo cikin wasu bukkoki da kuma babura sama da 13.
Kakakin, ya kara da cewa, majiyoyi da dama sun bayyana cewa ‘yan ta’addan ne ke da alhakin kai hare-hare da garkuwa da mutane a wasu yankuna na karamar hukumar Birnin Gwari da Igabi da kuma Giwa.
Daraktan ya ce rundunar ta sake kai wasu hare-hare ta sama a ranar 2 ga watan Yuni, 2024, inda suka lalata sansanin kasurgumin dan ta’adda Alhaji Iliya da yaransa a tsaunin Zango da ke karamar hukumar Kankara a Jihar Katsina.
Ya ce “bayan kai harin, hotunan sun nuna yadda aka yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda da dama a yankin”.
Ya bayar da tabbacin cewar za su ci gaba da kai hare-hare don kawar da ‘yan ta’adda da kuma wanzar da zaman lafiya a yankunan.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
