Connect with us

News

Shugaba Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi a safiyar gobe Laraba.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai yi wa ‘yan Najeriya jawabi a wani ɓangare na Ranar Dimokuraɗiyya a gobe Laraba.

Advertisement

Wata sanarwa da fadar sugaban ƙasar ta fitar ta ce Tinubu zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe, tana mai shawartar dukkan gidajen rediyo da talabijin su ɗauki jawabin daga gidan talabijin na ƙasa NTA da kuma gidan rediyon tarayya na FRCN.

Rikicin Masarauta :  Aminu Ado Bayero ya umarci Hakimai su shirya hawan Sallah Babba

Ana sa ran shugaban zai yi magana kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekara ɗaya da hawa mulki bayan rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Advertisement

Kazalika, ana sa ran zai taɓo batun mafi ƙarancin albashi da ake ta taƙaddama a kai tsakanin gwamnatinsa da kuma gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago, abin da har ya jawo yajin aiki na kwana ɗaya.

Babu tabbas ko shugaban zai sanar da sabon mafi ƙarancin albashin bayan Naira Dubu 62,000 da gwamnati ta sanar a wannan makon, wanda kuma ƙungiyoyin NLC da TUC suka yi watsi da shi kuma suke neman Naira Dubu 250,000.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending