News
Wani gini na makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano ya kone kurmus
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani gini a makarantar kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano wato Kano State Polytechnic ya kone kurmus sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar Talata.
Rahotanni na nuni da cewa gobarar ta lakume daukacin sashen fasaha da masana’antu na kwalejin kimiyya da fasaha wato Arts and Industrial Department
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar laraba a matsayain ranar hutu
Yayin da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Yusif Abudullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.
Ya kara da cewa ba za a iya tantance bayanan asarar da aka samu nan take ba saboda ana ci gaba da bincike.
Duk da haka, ya yi alkawarin bayyana abinda ya faru bayan kammala binciken.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
