Connect with us

News

Kimanin ‘Yan Kasuwa 5,000 Ne Za Su Yi Asarar Shagunan Su A Jihar Kano.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kimanin ‘yan kasuwa 5,000 ne za su yi asarar shaguna a kusa da masallacin Idi a Kano, biyo bayan sanarwar dakatar da su da hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta yi musu.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Yakubu Muhammad ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wata ganawa da manema labarai.

Rediyon Freedom Ta Rasa Gogaggen Dan Jarida:   Ibrahim Danuwa Rano Yayi Murabus Bayan Shekaru 16 Yana Aiki

Hukumar KNUPDA ta bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga ‘yan kasuwa a masallacin da ke kan titin IBB a cikin babban birnin Kano da su bar yankin ko kuma su fuskanci fushin doka.

 

Muhammad ya baiyyana cewa shekaru 18 da suka gabata Marigayi Galadima na Kano, Alhaji Tijjani Hashim ne ya raba musu wurin ta hannun Masarauta.

Advertisement

Ya ce gwamnatocin da suka gabata a jihar sun ga ya dace a bar ‘yan kasuwar su ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin.

“Muna da yawa a nan, galibin mu matasa ne , ta yaya za ku yi kokarin raba wadannan mutane da kasuwancinsu, kun san hakan zai haifar da hatsari ga jihar,” in ji shi.

Muhammad ya ce ’yan kasuwar ba su fahimci dalilin da ya sa gwamnati ke aika musu kaya ba duk da cewa suna bin doka da oda kuma suna ba da gudummawar kudaden shiga da jihar ke samu a cikin gida.

“Har yanzu muna kokarin ganin mun shawo kan hakikanin laifin da muka aikata wanda ya sa KNUPDA ta ke sharin fatattake mu daga inda muke gudanar da sana’o’inmu na halal domin kula da iyalanmu.

“Mun goyi bayan wannan gwamnati. Mun zabe shi a lokacin zaben 2023. Mafi kyawun gudunmawa da wannan gwamnati za ta iya ba mu shi ne ta ba mu damar ci gaba da kasuwancinmu a Masallacin Idi,” in ji shi.

Ya kuma bukaci Gwamna Abba Yusuf da su shiga tsakani domin ceto sana’o’insu daga rugujewa.

Advertisement

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Da aka tuntubi wata majiya a KNUPDA da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa hukumar ta umurci ‘yan kasuwar da su bar wurin saboda suna mamaye wurin ba bisa ka’ida ba.

“KNUPDA na ganin ‘yan kasuwar ba su nemi izini daga gare ta ba kafin su fara kasuwanci a wurin. Don haka ne hukumar ta bayar da sanarwar janyewar su . Suna aiki ba bisa ka’ida ba a wurin.”

 

 

 

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending