Connect with us

News

Nijeriya Za Ta Iya Biyan Mafi Karancin Albashi Da Kudaden Da Aka Kwato Daga Hannun Barayin Gwamnati  —Lauya Falana

Published

on

DAGA  YASIR SANI ABDULLAHI 

Lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, SAN, ya ce gwamnatin tarayya da  Gwamnonin jihohi suna da ikon biyan mafi karancin albashi muddin aka kwato kudaden da aka wawashe.

Advertisement

Falana ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da gidan Talabijin na Channels, wanda Jaridar INDA RANKA ta sanyawa ido.

“Gwamnatocin jihohin da ke cewa ba su da kudin da za su biya, kudin na nan.

Advertisement

Kotun  Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Sarki Na 15 Naira Miliyan 10.

“Abin da suke bukata, ciki har da Gwamnatin Tarayya, shi ne tattara manufofin siyasa don tattarawa da kuma kwato kudaden da aka sace ko aka boye daga asusun tarayya,” in ji shi.

Haka zalika Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa  har yanzu kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya sun kasa cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi bayan da ma’aikatan suka ki amincewa da tayin N62,000 da gwamnatin ta yi.

Advertisement

A taron karshe da kwamitin uku kan sabon mafi karancin albashi ya yi a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja, ma’aikata sun rage bukatarsu zuwa N250,000 daga N494,000, yayin da gwamnatin tarayya ta kara tayin daga N60,000 zuwa N62,000.

Za a iya jira mafi karancin albashin ma’aikata har zuwa ranar 2 ga watan Yuli saboda majalisar dokokin kasar na hutu.

Advertisement

A yayin tattaunawar, Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi kasar su saka siyasa cikin  biyan mafi karancin albashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending