News
Siyasa Ta Lalata Mana Zamantakewa Har Murna Ake Idan Musifa Ta Samu Mutum —Barista Ishaq
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani Malamin Addinin musulunci, Barista Ishaq Adam, ya bayyana rashin jin dadinsa akan yadda al’ummar musulmi ke murna idan wata musifa ta afkawa dan uwansu, kawai saboda saɓanin ra’ayin kwallon ƙafa, ko siyasa ko wata mu’amala ta yau da Kullum .
Barista ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook na Karatuttukan Malaman Musulunci.
Inda ya bada misalin da sace mahaifiyar mawaƙin siyasa ne Dauda Adamu Rarara, da yace ya ga wasu sai murna suke yi, wanda hakan ba koyarwa Addinin musulunci bane,
Haka zalika ya ce a Addinin musulunci ana so duk abinda ya samu musulmi to dan uwansa musulmi yaji cewar kamar shi abin ya shafa.
Malamin ya ƙara da cewa, tsarin mulkin Demokradiyya ya sanya abubuwa sun lalace,
Wanda kamata yayi idan wata musifa ta samu mutum, a taimaka masa ko da addu’a ne, domin babu wanda ya tsira daga shiga irin wannan jarabawa.
NasaraRadio
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
