Connect with us

News

Jami’yyar Adawa Ta Labour Ta Karɓe Mulki Bayan Shekaru 14 A Birtaniya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Jami’yyar adawa ta Labour ta kawo karshen shekara 14 na mulkin Jam’iyyar Conservative a kasar Birtaniya.

Advertisement

Kazalika Labour ta kwace kujerar tsohuwar fira ministar Birtaniya Liz Truss da ke wakiltar mazabar Norfolk ta Kudu maso Yamma a Majalisar Dokokin kasar.

JAMB Ta Bankaɗo Dalibai 3,000 Na Bogi Da Suka Kammala Karatu Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Jam’iyyar Labour ta kafa tarihin doke Conservative ne bayan zaben ranar 5 ga watan Yuli inda ta samu rinjayen kujeru a majalisar dokokin kasar.

Advertisement

A yayin da zaben ke ci gaba da kirga kuri’u, Fira Minista Rishi Sunak, ya amsa shan kayi.

Ya sanar da cewa, “na dauki laifin wannan faduwa da muka yi.”

Advertisement

Da wannan shan kaye, Rishi Sunak zai sauka daga kujerar Fira Ministan, wadda Shugaban Jam’iyyar Labour, Keir Starmer, zai dare domin kafa sabuwar gwamnati.

Da yake jawabi, Starmer ya ce, “yau mun bude wani sabon babi a Birtaniya.”

Advertisement

Ya ci gaba da cewa, “nasarar zabe ba daga sama take fadowa ba, sai da yaki da gwagwarmaya.

“Shi ya sa a wannan karo Jam’iyyar Labour ta kai ga narasa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending