Connect with us

News

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Mayar Da Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers Yan  Ɓangaren Nyeson Wike

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta soke dakatarwar da wata babbar kotun jihar Rivers ta yi wa ‘yan majalisar dokokin jihar na bangaren Ministan birnin taraiya Abuja Nyeson Wike a watan Mayun wannan shekara ta 2024.

Advertisement

Jaridar premium Times ta ruwaito cewa A wancan lokaci dai kotun ta jihar Rivers ɗin ta haramtawa wadannan yan majalisar su 24 shiga zauren Majalisar su gudanar da duk wani zama da sunan majalisar dokokin jihar ta Rivers, sannan ta hana Martin Amaewhule baiyana kan shi a matsayin kakakin majalisar.

Kotun ta yi haka ne saboda ƙara da aka shigar ake bukatar ta aiyana ƙwace kujeru su na majalisar saboda sauya sheƙa da suka yi daga PDP zuwa APC, saidai wannan kotun ta ɗaukaka ƙara saɓanin wancan hukunci ta yi inda ta ce Martin Amaewhule da yan majalisar 24 na ɓangaren Wike su ne halastattun yan majalisar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending