News
BIDIYO: Wasu Matasa ‘Yan Masarautar Ƙaraye Sun Far Wa Wakilin Sarki Sunusi Ya Yin Da Ya Ziyarci Masarautar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu matasa da suka fusata a karamar hukumar Karaye ta jihar Kano sun kori wakilin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis.
Daily Trust ta ruwaito cewar wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, lamarin ya faru ne a lokacin da wakilin sarkin ke kan hanyarsa ta zuwa fadar tare da shugaban karamar hukumar, Wada Nababa Tudun-Kaya.
Zargin Cin Hancin N15m: Kotu Ta Kori Karar Da Sarakunan Suka Yi Na Hana EFCC Bincikesu.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Alhaji Ibrahim Abubakar II, tsohon Sarkin Karaye, yana daya daga cikin sarakuna biyar da gwamnatin Kano ta kora.
Shaidan ya ce, “Abin da ya faru shi ne wakilin Sarkin ya shigo gari, shugaban riko ya karbe shi da farko. Don haka, a hanyarsu ta zuwa yin rajistar kasancewarsa, wasu fusatattun matasa sun far musu.
“Kun san har yanzu muna son masarautun mu da aka rusa kuma har yanzu ba mu farfado daga abin da ya faru ba. Abin da ya faru ba tashin hankali ba ne ko kadan amma daya daga cikin gilashin motarsu ya lalace.
“Akwai ofishin ‘yan sanda a gaban fadar Karaye; wanda hakan ya taimaka wajen shawo kan lamarin yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa taron al,umma.”

