Connect with us

Politics

Allah Ne Kadai Zai Iya Magance Rikicin Siyasar Da Ke Tsakanin Gwamnan Jihar Ribas Da Nyesom Wike —Shehu Sani

Published

on

Shehu Sani,Siminalayi Fubara,Nyesom Wike

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan rajin kare hakkin jama’a kuma tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ta takwas, Sanata Shehu Sani, ya ce Allah ne kadai zai iya magance rikicin siyasar da ke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara tsohon ubangidan siyasa, Nyesom Wike.

Advertisement

Arise Tv ta ruwaito cewa Kalaman Sani ya zo ne a daidai lokacin da wata kungiyar Neja Delta, 21st Century Youths of Niger Delta and Agitators with Conscience, suka bayyana shirun da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi game da rikicin siyasa da ya dade a Rivers a matsayin abin damuwa,

Za A Turawa Shugaba Tinubu Kudurin Kafa Hukumar Kula Da Arewa Maso Yamma 

Sani, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na  X, ranar Talata, ya ce, “An bar jihar Rivers a hannun Allah domin magance matsalar.”

Advertisement

A baya-bayan nan dai rashin jituwar da ke tsakanin Gwamnan da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja ta yi kamari inda ake gwabza fada a zauren Majalisar tsakanin bangarorin da ke biyayya ga mutanen biyu.

‘Yan majalisar masu goyon bayan Wike a ranar Litinin sun umarci Fubara da ya sake gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2024 a cikin kwanaki bakwai.

Advertisement

Sai dai ana kallon hakan a matsayin wani share fage na fara yunkurin tsige gwamnan, domin masana harkokin siyasa sun yi hasashen cewa gwamnan ba zai bi umarnin ba

Fadan Fubara/Wike ya kai ga fitowar shugabannin majalisar dokokin jihar guda biyu, Martin Amaewhule da kuma Victor Oko-Jumbo, wadanda ke goyon bayan Wike da Fubara, bi da bi.

Advertisement

Wata sanarwa da shugaban kungiyar Niger Delta Izon Ebi ya fitar ta yi Allah wadai da shirun da Tinubu ya yi kan rikicin jihar Ribas. An yi zargin cewa shugaban ya ki kiran Wike ya ba da oda.

Kungiyar ta yi gargadin cewa bai kamata shugaban kasa ya kyale yunkurin Wike na neman iko a siyasance na gwamna da hukumomin gwamnati ba.

Advertisement

Ebi ya ce, “Rashin zaman lafiya a jihar Ribas tabbas zai haifar da rashin zaman lafiya a yankin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending