News
Tsoratar Da Mu Aka Yi Da Ƙara Kuɗin Fetur, Muka Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na Dubu ₦70 – Ƙungiyar Ƙwadago
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ya bayyana cikakkun bayanai game da yarjejeniyar da ta cimma da Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Shugabannin NLC sun amince da tayin ₦70,000 domin daƙile yiwuwar ƙarin farashin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ke shirin yi.
Da farko, ƙungiyar ƙwadagon ta nemi ƙarin albashi mafi girma, amma ta yanke shawarar yin rangwame domin kaucewa ƙara wahalar da ‘yan Nijeriya.
ANAWA DIMUKURADIYYA KARAN TSAYE: Ayar Tambaya Game Da Tsige Ndume Da Majalisa Ta Yi
An cimma wannan matsaya ne bayan taron gaggawa na NEC da aka gudanar a Abuja, bayan wani taro da aka yi da Gwamnatin Tarayya a ranar 18 ga Yuli, 2024.
Taron, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta, ya haifar da tattaunawa mai zurfi wanda ya kai ga amincewa da albashi mafi ƙaranci na ₦70,000. Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, cikin wata sanarwa, ya yaba da jajircewar shugabannin ƙungiyar wajen gudanar da tattaunawar albashi.
Leadership ta ruwaito cewa NEC ta NLC ta amince da tayin Shugaban Ƙasa na ₦70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da kuma wa’adin duba shi bayan shekaru uku. Sun kuma buƙaci cikakken bin dokar mafi ƙarancin albashi na ƙasa da zarar ta zama doka a Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Duk da wannan amincewa mai wahala, NLC ta jaddada ƙudirinta na karewa da inganta hakkokin ma’aikatan Nijeriya, kuma ta kira ‘yan Nijeriya gaba ɗaya su haɗa kai wajen riƙe shugabanni kan alhakin irin wannan sadaukarwa da ta rataya a wuyansu.
