Connect with us

News

Allah Yasa Zanga-Zangar Da Za A Yi Ta Kawo Ƙarshen Gwamnatin Shugaba Tinubu – Sheikh Murtala Bello

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani Malamin addinin Musulunci da ke zaune a Sakkwato, Sheikh Murtala Bello, ya yi addu’ar fatan Allah ya sa zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin kasar ya kawo ƙarshen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Advertisement

WIKKI TIMES ta ruwaito cewa Malamin ya caccaki Malaman addinin Musulunci da suka ce yin zanga-zangar babu shi a tsarin addinin Musulunci.

Gwamnatin jihar Katsina na shirin samar da Dokar “Iddah” ga matan Jihar

A rahotanni da suka bayyana an ji Manyan Malaman Addinin Musulunci irin su Dr Sani Rijiyar Lemo da Sheikh Aminu Daurawa sun fito sun nuna kin amincewar su tare da hana Musulmi shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin kasar.

Advertisement

Inda Suka yi nuni da cewa hakan ya sabawa addinin musulunci, kuma zai iya kawo rashin zaman lafiya da asarar rayuka da dukiyoyi a kasar kamar yadda yake faruwa a ƙasashe Libya, Sudan da sauran wurare.

Shi kuma a nashi talatin ta wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a lokacin da yake gabatar da wa’azi, Sheikh Bello ya ce akasarin jihohin yankin Arewa maso Yamma suna fuskantar firgici da ba za a iya kwatantawa ba sakamakon ayyukan ta’addanci da ƴan bindiga kamar yadda yake faruwa a Sudan da Libya.

Advertisement

In ba a Manta ba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi kira a ranar 11 ga watan Yuli, inda ya yi kira ga musulmi masu imani da su guji shiga zanga-zanga, yana mai cewa hakan ka iya haifar da illa fiye da alheri.

Shehin Malamin na Kano ya ce wasu masu yin barna na iya yin amfani da damar wajen shirya rashin zaman lafiya a kasar nan.

Advertisement

Amma kuma a nashi bangaren Sheikh Dr Ahmad Gumi, Shi kuma yace zanga-zanga lumana hanya ce mai kyau don isar da wahalar da al’umma ke ciki gwamnati .

Yayin da yake gabatar da lakca a Kaduna, Gumi ya yi kira ga matasa da su daina lalata dukiyoyi da barna da sunan zanga-zanga.

Advertisement

Sai dai Sheikh Sani Rijiyan Lemo ya bayyana cewa babu tabbacin za a yi zanga Zanga-Zangar cikin lumana

Ya ba da misali da Libya, inda ya ce an fara ne a matsayin zanga-zangar lumana amma ta rikide zuwa wani yunkuri na tashin hankali. Don haka ya ba da shawarar a guji zanga-zangar.

Advertisement

In ba a Manta ba dai a makon da ya gabata ne al’ummar Najeriya suka shirya fita Zanga-Zanga a karshen wannan wata domin kawo ƙarshen wahalhalu rayuwa da ƙasar ke fuskanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending