Connect with us

News

Fasinjoji 119 Sun Tsallake Rijiya Da Baya Sakamakon Fashewar Tayoyin Jirgi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Max Air NGL1649, Boeing 737 mai lamba 5N-ADB ya tsallake rijiya da baya a jiya Lahadi

Jaridar Zuma Times ta ruwaito cewa Jirgin wanda ke ɗauke da fasinjoji 119 da ma’aikatan jirgi 6 yana tsaka da shirin tashi daga filin jirgin sama na Yola jihar Adamawa inda zai nufi Abuja sai kwatsam aka ji duka tayoyin jirgin guda huɗu sun yi bindiga sun fashe lamarin da ya jawo dole aka fasa tafiyar aka sauke fasinjojin.

Joe Biden Ya Janye Daga Takarar Shugaban Amurka 

A wani Labarin Kuma, anji cewar Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar rundunar sojin sama (NAF) ya yi hatsari a yankin karamar hukumar Igabi dake jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a wani muhalli dake daura da hedikwatar horon sojojin sama dake Mando, karamar hukumar Igabi, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya rawaito.

Rahotanni sun nuna cewar karfe 7 na safe ya kamata matafiyan su tashi zuwa Yola amma sakamakon Fashewar waɗannan tayoyi sai karfe biyu na dare sannan suka sami damar ɗagawa zuwa Yola.

Advertisement

Mazauna yankin sun shaidawa Channels Television cewa jirgin ya yi hatsarin ne da safiyar ranar Litinin a kauyen Taimi dake kusa da Rigachikun.

Sai dai, a wani jawabi da rundunar sojin sama ta fitar ta bakin kakakinta, Edward Gabkwet, ta bayyana cewa jrigin da ya yi hatsari ba mai saukar ungule bane, wani jirgi ne na musamman mai sarrafa kansa ba tare da direba ba (UAV).

Gabkwet ya bayyana cewa, “jirgin rundunar NAF mai sarrafa kansa (UAV) ya samu tangarda yayin da ya ke sararin samaniya domin gudanar da wani aiki. Lamarin ya faru ne a daura da kauyen Rumji mai nisan Kilomita 15 daga sansanin sojin saman.

 

 

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending