News
Zanga zanga: Shekara Ɗaya tayi kaɗan a auna ƙwazon Gwamnati – Ministan tinubu
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Karamin Ministan Albarkatun Ruwa Kuma tsohon kwamishinan yada labarai na Jahar Sokoto Barista Bello Goronyo ya yi kira ga waɗanda suka shirya zanga-zanga akan halin yunwa da ake fuskanta da su janye matakin da suka ɗauka, yana mai cewa shekara daya ba ta isa a yanke hukunci ga Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba.
Jaridar daily trust ta rawaito a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da Gwamnatin Jihar Sokoto ta kira domin tattauna batun zanga-zangar da aka shirya yi, Goronyo ya yi nuni da cewa waɗanda suka shirya zanga-zangar fa ba za ta cutar da Shugaban ƙasa bane face al’ummarmu.
Ya ce, “Wadannan mutanen ɓata gari ne, sun shirya hakan ne don su hargitsa kasar a matsayinmu na al’umma ɗaya,
Yana mai cewa ba wai Shugaban kasa suke hari ba, a,ah suna harin al’ummar ƙasar ne, suna son su hargitsa mu kamar kasashe irin su Sudan da har yanzu suke cikin wani hali Kuma bamasan Nigeria ta Shiga irin wannan halin
Shugaban ya riga ya ambata tun farkon Gwamnatin sa cewa kasar na cikin wani mawuyacin hali, da gadar basussuka da dama daga gwamnatocin da suka shuɗe, amma kuma duk ya karɓi hakan da niyyar Kawo gyara, don haka shekara ɗaya da wata biyu ba su isa a tantance ƙwazon sa ba, a matsayin Gwamnatin da ta gaji basussuka”.
A cewar Goronyo Gwamnati na yin duk mai yiwuwa don dakile yunwa da rashin tsaro a kasar.
Gwamanti na bin duk hanyoyin da suka dace domin kawo karshen rashin tsaro amma ba za mu iya bayyana su ba saboda suna buƙatar sirri, sai dai wadanyda abin ya shafa sun san da haka,” inji shi.
Ya ƙara da cewa a karon farko Gwamnati mai ci ta samar da Dam-dam na ruwa domin noman rani, inda ya ce yanzu haka akwai Dam guda 408 da za a yi amfani da su wajen noman rani.
Ya kuma yabawa Gwamnati bisa kafa hukumar raya Yankin Arewa maso Yamma da Ma’aikatar kiwo da yayi.
