Connect with us

News

Za A Daure Duk Shugaban Karamar Hukumar Da Ya Yi Wadaka Da Kudin Kananan Hukumomi –Gwamnatin Tarayya

Published

on

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tunibu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayya ta yi tsauraran gargadi ga shugabannin kananan hukumomi tare da barazanar garkame duk wanda yake tafka almundahana da kudaden da aka ware daga asusun tarayya domin kananan hukumomi.

Advertisement

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi wannan gargadi a lokacin wata lakca ta tunawa da cika shekara 17 na kungiyar kare hakkin dan Adam ta Najeriya (HURIWA) a Abuja kamr yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito

Fagbemi ya jaddada cewa shugabannin kananan hukumomi ba su da kariya daga daukar mataki, kuma za su fuskanci daurin kurkuku idan suka yi amfani da kudaden da aka ware don ci gaban yankunan su ba daidai ba.

Advertisement

Ya bayyana cewa, “Shugabannin majalisar kananan hukumomi ko kansiloli, ba su da kariya, don haka dole ne su zabi tsakanin sarrafa kudaden ta yadda ya kamata ko kuma ta yadda suka ga dama Zabin na su ne.”

Ya kuma jaddada muhimmancin dawo da ayyuka a karkara kamar gine-ginen hanyoyi don inganta ci gaban yankuna da tsaro.

Advertisement

“Idan akwai zababbun shugabannin kananan hukumomi, za mu iya rage matakin rashin tsaro da muke da shi a Najeriya a yau,” in ji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar amfani da Kotun Koli don tabbatar da ikon kananan hukumomi saboda zaton adawa daga majalisun jihohi.

Advertisement

Ya nuna cewa duk wani kakakin majalisar jiha da ya goyi bayan wannan shiri ba zai iya kammala wa’adinsa ba ko kuma sake samun zaben kujerar sa.

Fagbemi ya lura cewa fiye da shekaru ashirin, gudanar da kananan hukumomi a Najeriya ya lalace saboda gwamnatocin jihohi suna kasa sauya kudaden da aka ware don kananan hukumomi.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro su guji tsare wanda ake zargi fiye da lokacin da kundin tsarin mulki ya tanada ba tare da samun umarnin kotu ba, yana gargadin cewa wadanda suka keta wannan dokar za su fuskanci hukunci da ya dace.

Jagoran HURIWA, Kwamared Emmanuel Onwubiko a taron, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta rage kudaden gudanarwa.

Advertisement

Ya danganta rashin tsaro a kasa da kuma karancin ayyukan yi ga cin hanci da rashawa, wanda ya ce yana haifar da zanga-zangar da ke tafe a fadin kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending