Business
Karya ake mana, bama sayar da ‘danyan mai – Dangote
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanin Dangote ya yi watsi da zargin da ake masa cewar yana sayar da ‘dayan man da ake ba shi ya tace a sabuwar matatarsa saboda matsalar da matatar ke fuskanta.
Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Reuters ya yi ne ya sanar da haka, inda yace kamfanin na fama da matsala saboda haka ba ya iya tace man da ake ba shi dalilin da ya sa shi sayar da ‘danyan man.
Wasu ‘Ya’ya Da Suka Fusata Sun Raunata Mahaifinsu Tare Da Kashe Dan Uwansu A Jigawa.
Sai dai cikin fushi, mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina ya yi watsi da zargin wanda ya bayyana shi a matsayin labaran karya.
Chiejina yace kamfanin na su ba shi da hurumin sayar da ‘danyan man da aka ba shi a Najeriya, kuma matatar su na aiki kamar yadda ya fara, saboda haka babu dalilin yin haka.
Kakakin kamfanin ya bukaci jama’a su yi watsi da rahotannin wanda ya danganta shi da masu kokarin batawa kamfanin su suna saboda adawar da suke da tace mai a cikin Najeriya da kamfanin ke yi.
Takaddama ta kaure a ‘yan kwanakin nan tsakanin kamfanin Dangote da na NNPC dangane da matatar su da kuma kin bai wa kamfanin isasshen danyan man da yake bukata domin gudanar da aikin sa.
Wannan takadadmar ce ta sanya Aliko Dangote gabatar da bukatar sayar ad matatar ga kamfanin NNPC saboda abinda ya kira adawar da yake fuskanta wajen gudanar da ayyukansa.