Connect with us

News

Zaben Kananan Hukumomi:  Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Kwaya Kafin Ba Su Damar Tsayawa Takara A Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, ta bayyana cewar za a yi wa ‘yan takara gwajin miyagun kwayoyi kafin ba su damar tsayawa takara.

Advertisement

Shugaban hukumar zaben jihar, Farfesa Sani Malunfashi ne, ya shaida wa manema labarai a Kano.

Ta Kashe Mijinta Mai Cutar Shanyewar Ɓarin Jiki, Ta Jefar Da Gawarsa A Kango

Rahotanni na nuni da cewa hukumar za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024.

Advertisement

Hukumar zaben ta kuma sanar da cewa haramun ne manna fastocin yakin neman zabe a ginin gwamnati, fada, da wuraren ibada, kuma za ta hana duk wanda ya keta wannan doka tsayawa takara.

Ana sa ran gudanar da zaben ne a kananan hukumomin jihar 44.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending