Connect with us

News

An Kama Sojan Da Ya Harbe Mai Zanga-Zanga A Zaria

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar Sojin Ƙasa a Nijeriya ta ce ta tsare wani jami’inta da ya harba bindiga don gargaɗi ga masu zanga-zanga a garin Zariya  na jihar Kaduna, inda harsashin ya samu wani yaro tare da halaka shi.

Advertisement

A wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, ta bayyana cewar a ranar 6 ga Agusta Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta samu kiran neman agaji saboda wasu ɓata-gari sun taru a Samaru, suna ƙona tayoyi a kan hanya da jifan jamia’n tsaro da duwatsu.

Zaman Mutum Shi Kadai Na Wani Dan Lokaci Zai Iya Rage Masa Gajiya Da Kuma Damuwa

Hakan ne ya sa rundunar ta tura jami’anta zuwa wajen da niyyar tarwatsa ɓata-garin da kuma tabbatar da an bi dokar hana fita da gwamnatin Jihar Kaduna ta saka.

Advertisement

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan zuwan sojoji wajen, ɓata-garin suka yi yunƙurin kai musu hari, abin da ya sanya wani soja harba bindiga don gargaɗinsu, amma tsautsayi ya sanya harsashin ya faɗa kan wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Ismail Mohammed wanda ya kuma rasu.

“Bayan bayyana matuƙar ɓacin rai game da lamarin, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa Laftanal Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya aike da babbar tawaga ƙarƙashin Babban Kwamandan Runduna ta 1 Manjo Janar Lander Saraso don yin ta’aziyya ga iyayen yaron da aka kashe,” in ji sanarwar.

Advertisement

Sanarwar ta kuma ce tuni aka tsare tare da fara binciken sojan da ya yi harbin

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending