Connect with us

News

Ba Mu Umurci ‘Yan Bautar Ƙasa Su Sabunta Asusun Bankinsu  Ba – NYSC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar NYSC ta bayyana cewa ba ta umarci ƴan bautar ƙasa su sabunta asusun bankinsu don karɓar mafi karancin albashin N70,000 ba.

Advertisement

Za a iya tuna cewa, gwamnatin da ta gabata ta daidaita alawus ɗin ƴan bautar ƙasa da albashi mafi ƙanƙanta.

‘Yan sanda sun yi martani kan ‘yan bindigan da ke baje-kolin kuɗin fansa a Yanar Gizo

Hukumar ta NYSC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a, na hukumar Mista Eddy Megwa, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Advertisement

A cewar Megwa, bayanan da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cewa ƴan bautar ƙasa su sabunta asusun bankinsu don biyan wannan albashi, ƙarya ce tsagwaronta.

Ƴan bautar ƙasa, iyaye, da jama’a su sani cewa babu wani umarni da aka samu daga duk wani sashe na gwamnati mai alhakin harkar albashi. Saboda haka, ba zai yiwu NYSC ta fitar da wani umarni kan haka ba.

Advertisement

“Ƴan bautar ƙasa sun san hanyar da aka amince da ita wajen isar da saƙo a cikin shirin, saboda haka su yi watsi da wannan umarni na ƙarya da ake yadawa.

“NYSC ba ta fitar da wannan sanarwa ba, don haka tana jan hankalin ‘ƴan bautar ƙasa da su guji wannan jita jita da masu yaɗa ƙarya domin a yaudare su,” in ji shi.

Advertisement

Megwa ya kuma gargadi masu rubuce-rubuce a shafukan yanar gizo da kafar sada zumunta da su daina fitar da bayanan da suka shafi harkokin gudanarwar NYSC ba tare da izini ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending