Connect with us

News

‘Yan sanda sun yi martani kan ‘yan bindigan da ke baje-kolin kuɗin fansa a Yanar Gizo

Published

on

Yan Sanda Sun Yi Martani Kan 'Yan Bindigan Da Ke Baje kolin Kuɗin Fansa A Yanar Gizo 
Matsalolin 'yan bindiga masu garkuwa da mutane na daga cikin abubuwan da ke damun arewacin Nijeriya.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta  mayar da martani dangane da hotunan wasu ‘yan bindiga da ke baje-kolin kuɗin fansa a shafukan sada zumunta.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya yi martanin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Advertisement

An Yanke Wa Wasu Sojoji 24 Hukuncin Daurin Shekaru 120 A Gidan Wakafi

Ƙorafin da wani mai wallafa labarai dangane da tsaro ZagazOlaMakama ya yi a shafinsa na X inda ya wallafa hotunan ‘yan bindigan tare da cewa yanzu har ta kai suna nuna kuɗin fansar da suke karɓa,

“Ba za mu iya kama duka masu laifi a lokaci guda ba. Aƙalla a yaba mana dangane da waɗanda muka kama. Muna kama su a kullum, kuma masu yawa,” in ji Adejobi a martanin da ya mayar.

Advertisement

“Jami’an soji da ‘yan sanda na iya bakin ƙoƙarinsu. Ya kamata a rinƙa gani tare da yaba wa ƙoƙarin jami’an. Akwai buƙatar mu haɗa kanmu baki ɗaya domin magance matsalolin tsaro da wasu matsalolin a Nijeriya. Akwai tabbacin cewa babu wani mai laifi da zai ci bulus ba tare da an hukunta shi ba,” kamar yadda Adejobi ya ƙara da cewa.

Duka waɗannan na zuwa a daidai lokacin da a ‘yan kwanakin nan aka ga wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suna amfani da shafukan sada zumunta tare da tambayar lambobin asusun ajiya na jama’a domin ba su na goro.

Advertisement

Matsalolin ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane na daga cikin abubuwan da ke damun arewacin Nijeriya.

Yan bindigar suna da sansanoni a dazukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, da Neja, inda suke kai mutanen da suka sace, ciki har da ɗalibai daga makarantu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending