News
Muna Allah-wadai Da Kudaden Da Aka Sanyawa ‘Yan Takarara A Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano —Kungiyar WAI
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam, yaƙi da rashin adalci dama bibiya akan shugabanci na gari wato War Against Injustice (WAI), ta yi kakkausar suka ga sanarwar da Hukumar Zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta sanya naira miliyan 10 a matsayin kudin tsayawa takarar shugabancin karamar hukuma yayin da kowane mai takarar kansila zai biya naira miliyan 5.
Wannan kuɗaɗen zai ta hana ƴan ƙasa yancin shiga harkar siyasa tare da ci gaba da cin hanci da rashawa a harkokin mulki.
Da Dumi-Dumi: Kano Ta Sanya N10m Matsayin Kudin Tsayawa Takarar Shugabancin Karamar Hukuma
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Babban Darakta, Kungiyar comrade Umar Ibrahim Umar ya turawa da Jaridar INDA RANKA
Sanarwar ta kara da cewa Kudaden da ya wuce gona da iri zai takaita shiga ga masu hannu da shuni da wadanda gurbatattun ‘yan siyasa da ubangida ke marawa baya, wanda hakan zai kawo cikas ga dimokuradiyya da wakilci na gaskiya.
Muna kira ga hukumar KANSIEC da ta sake duba wannan matakin, duba da irin halin kuncin da ake ciki a fannin tattalin arziki, sannan kuma ta baiwa duk wani mai son tsayawa takara damar shiga ba tare da tabarbarewar kudi ba.
Wannan yana tabbatar da cewa shugabannin da suka cancanta sun fito, masu wakiltar muradun jama’a da gaske.
Dole ne KANSIEC ta fifita dimokuradiyya da adalci fiye da samun kudi, gina wakilai da rikon amana da yiwa al’ummar jihar Kano hidima.
