News
Wani Mai Shayi ya kashe Barawo har lahira bayan zarginshi da Satar Biredi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani Mai Sana,ar sayar da shayi mai Suna Abdulrashibu Ya’u dan kimanin shekaru 40 a kauyen Sararai da ke garin Tsada a karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa ya yiwa wani matashi mai Suna Hassan Garba dan shekara 20 dukan tsiya har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ya’u ya zargi Garba da satar masa biredi, da taliyar Yan yara, da kuma fetur da yake amfani dashi wajen Sana,ar tasa.
Da samun rahoton ‘yan sandan sun tura jami’ai wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke wanda ake zargin, yayin da aka garzaya da wanda aka halaka zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa,DSP Lawan Shiisu Adam ya ce a lokacin da yake amsa tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse, Ya’u ya amince da aikata laifin, inda ya bayyana cewa satar da Garba ya yi masa itace ta kara fusata shi, kuma a baya ya sanar da iyayensa, amma ba a dauki wani mataki ba.
Ya ce a fusace, Ya’u ya daure Garba da igiya, ya yi masa duka da sanda har ya kai ga mutuwarsa.
Makwabta sun ba da rahoton jin kukan Garba na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da jami’an ‘yan sanda suka iso.
Yace bayan kammala bincike, za a gurfanar da Ya’u a gaban kotu domin ya fuskanci shari’a.
