Connect with us

News

Sabon kwamishinan Yan Sanda na Akwai Ibon Ya Rasu bayan Anyimasa Aikin Kansa

Published

on

1724935397706

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

wamishinan Yan Sanda na jihar Akwa Ibom Waheed Ayilara ya rasu bayan watanni shida da kama aiki 

 

Advertisement

Ayilara, ya zama kwamishinan ƴan Sanda na jihar a watan Fabarairu, ya rasu ne a yayin da ake yi masa aiki a asibitin jihar Legas.

 

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta rawaito Kwamishinan ya rasu ne  awanni kadan bayan halartar bikin kammala aiki da na zagayowar ranar haihuwa ga wasu manyan jami’an ‘Yan Sanda da ya gudana a Jahar Legas a jiya Laraba.

 

Advertisement

An rawaito cewa , ya rasu da safiyar yau Alhamis a asibitin koyarwa na jihar Legas inda likitoci ke yajin aiki.

 

Advertisement

Mamacin dai ya na fama da matsalar ciwon Kansa, inda aka yi masa aiki a safiyar ranar.

 

Advertisement

Sai dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Legas, Benjamin Hundeyin ba a daidai lokacin da ake hada rahoton.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending