News
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki Ya Sanar Da Dage Ranakun Komawa Makarantu A Fadin Jihar
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Gwamnatin Jihar Edo dake yankin kudu maso kudancin ƙasar nan tabi Sahun Takwararta Jihar Kano na dage Komawa Makarantun Primary da Secondary da za,ayi a Ranar Litinin dinnnan.
BBC Hausa ta rawaito gwamnatin jihar ta sanar da dakatar da komawa makarantun har sai abin da hali ya yi sakamakon ƙarin farashin litar man fetur.
Cikin sanarwar da matakin babban sakataren ma’aikatar ilimin ta jihar, Ojo Akin-Longe, ya fitar ranar Asabar, ya ce matakin ya zama wajibi sakamakon halin da iyayen Yara ke ciki bayan ƙarin kuɗin man fetur da wasu ƙarin matsaloli.
Jaridar Inda ranka ta rawaito cewa wannan ya biyo bayan Karin farashin litar Man Fetur da Gwamnatin Tarayya tayi Kasa da mako guda.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
