News
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Murabus Din Ajuri Ngelale Mai Magana Da Yawun Sa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amshi takardar daga Ajuri Ngelale, mai magana da yawunsa kuma wakilin shugaban kasa na musamman kan harkokin sauyin yanayi, inda ya sanar da shi murabus dinsa saboda wasu dalilai na kashin kansa da kuma lafiya sa .
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Asabar ta ce shugaban ya amince da dalilan Ajuri Ngelale na murabus din.
Da Dumi Dumi : Gwamnatin Jihar Kano Ta Soke Komawa Makaranta Ranar Litinin
Yayin da yake mika addu’o’insa da fatan alheri ga Ngelale da iyalansa, shugaban ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa.
Ya lura da kokarin Ajuri Ngelale da sadaukarwa wajen yi wa al’umma hidima, ya kuma gode masa bisa gudunmawar da ya bayar, musamman wajen bada jawabai na kasa gaba daya da kuma jagorantar kokarin da ake yi kan ayyukan sauyin yanayi da sauran muhimman tsare-tsare.
