Connect with us

News

Hukumar NDLEA Ta Lalata Tabar Wiwi Mai Nauyin Sama Da Kilo 100,000 A Gonaki Daban-daban Masu Faɗin Kadada 51

Published

on

images

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar Hana Safara da Shan Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) ta ce ta lalata tabar wiwi mai nauyin sama da kilo 100,000 a gonaki daban-daban masu faɗin kadada 51 a Jihar Ekiti.

Advertisement

Hakan na cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi, a Abuja.

Mutane 48 Sun Mutu, Shanu 50 Sun Babbake Kurmus Yayin Da Tankar Mai Ta Fashe

Babafemi ya ce jami’an NDLEA tare da Sojojin Najeriya sun fita a ranar Laraba, 3 ga Satumba, suka yi dirar-mikiya a sansanoni uku cikin dajin Ise-Ekiti, da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ise/Orun.

Advertisement

Ya ce wuraren da aka kai farmakin sun haɗa da Aba Saalaja, mai wanda daji ne mai faɗin kadada 23 da Aba Paanu mai kadada 12 sai kuma Aba Arogunmatidi, mai faɗin kadada 16, duk a cikin dajin Ise-Ekiti na Jihar Ekiti.

Ya ce an kama mutum biyu a ranar Juma’a kan titin Toro-Jos, a Kaduna su na ɗauke da kilo 305 na wiwi, wadda suka ɓoye cikin wata mota J5, mai lamba YLA 682 XM.

Advertisement

Babafemi ya cigaba da cewa, an kama wani da kilo 18 na wiwi a garin Maƙarfin Jihar Kaduna.

“Sai kuma wasu biyu da aka kama kan hanyar Zaria zuwa Kaduna, suna ɗauke da ƙwayar Taramol 1300 duk a rana ɗaya.” Inji shi.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa A Jihar Kogi ma a ranar Laraba an kama Taramol ƙwaya 77,000 da sauran kwalaben muggan ƙwayoyi daban-daban.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending