News
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Biyan Alawus Ga Rashin Yanayi Mai Kyau A Makarantu Da Kuma Ƙarancin Albashi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ranar 5 ga watan Oktoban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar malamai ta duniya, inda ake yin duba tare da yin nazari kan halin da malamai ke ciki da kuma yanayin aikinsu da nufin samar da hanyar kyautata rayuwarsu.
Taken bukin na bana shi ne: “Malaman da muke bukata domin ilimin da muke so; Dole ne duniya ta tashi domin magance karancin malamai”
Zaben Kananan Hukumomi: Ba Abinda Rashin ‘Yan Sanda Zai Haifar —Gwamnan Ribas
Bikin na bana na so ne duniya ta mayar da hankali kan yadda za’a magance matsalar raguwar malamai, a kuma samar da hanyoyin da za’a kara yawansu a ko yaushe, kuma bikin na bana yazo ne a Najeriya a daidai lokacin da har yanzu ba’a biya wasu daga cikin malaman albashin su ba.
Malaman makarantu a Najeriya na fama da fargaba ta rayuwarsu yayin da kuma matsin tattalin arziki ke jefa malamai da yawa cikin mawuyacin hali inda albashin da ake biyansu ke karewa a cikin sati guda.
Kan wannan batun ne Jaridar INDA RANKA ta tattauna da wasu da cikin malam Makaranta
TRACK UP
Ranar Malamai dai na tunawa ne da bikin amincewa da kundin shawarwarin hukumar kula da Ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da ƙungiyar ƙwadago ta Duniya na shekarar 1966 dangane da matsayin malamai, wanda ya ajiye mizani game da haƙƙoƙi da nauyin da ke rataye a wuyan malamai da kuma ajiye wani tsari na matakin farko da na ƙaro ilimi da ɗaukar aiki da yanayin koyo da koyarwa.
To sai dai a kullum masu sharhi na aza laifin tabarbarewar ilimi kan hukumomi, su kuma hukumomin suna cewa suna iya kokarinsu domin inganta ilimi
A bana dai ana wannan biki ne a daidai lokacin da matsalolin malamai a Najeriya, ke ƙaruwa, ga kuma matsin tattalin arziki, duk kuwa da irin ƙoƙari da hukumomi ke cewa suna yi na kyautata ɓangaren ilimin, amma koken da malaman ke yi na ƙara fito da zahirin matsalolin, da ya kamata mahukunta su gaggauta magance su don samun nagartacciyar al’umma.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
