Connect with us

News

Gwamnatin  Tarayya Na Shirin Janye Harajin VAT Kan Magunguna

Published

on

Gwamnatin  Tarayya Na Shirin Janye Harajin VAT Kan Magunguna
Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kammala aiki a kan dokar ofishin shugaban kasa ta janye harajin sayen kaya (VAT) a kan magunguna da na’urorin kiwon lafiya.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a, Alaba Balogun, yace an kammala aikin daidaita yadda za’a aiwatar da dokar yanzu saura a wallafata.

Advertisement

An Daure Direba Shekara 15 A Gidan Yari Bisa Samunsa Da Laifin Kashe Jami’in KAROTA 

“Gaba mafi mahimmanci a dokar ita ce tabbatar da cewa hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS) da takwararta ta yaki da fasa kwabri na iya fara aiwatar da shirin daina cazar harajin VAT a kan magunguna da na’urorin kiwon lafiya,” a cewarsa.

A cewar sanarwar, wallafa dokar da aka hade hancin bangarorinta na nufin cimma daya daga cikin manufofin ma’aikatar, na sakarwa harkar kiwon lafiya mara.

 

Advertisement

 

 

VOA

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *