News
An Daure Direba Shekara 15 A Gidan Yari Bisa Samunsa Da Laifin Kashe Jami’in KAROTA
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kotu ta yankewa wani direba mai suna Kassim Hussain mai shekaru 27 hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari da kuma tarar Naira 500,000 bisa samunsa da laifin kashe wani jami’in KAROTA a lokacin da yake kokarin cire lambarsa.
Alkalin babbar kotun jihar Kano, Mai shari’a Maryam Ahmed Sabo, ta umurci Kassim Hussain da ya ci gaba da zaman gidan yari na tsawon shekaru 5 idan ya gaza biyan tarar Naira 500,000
Kwankwasiyya Na Fuskantar Rikici: Zan Bayyana Gaskiyar Kalar Jibrin Kofa – Aliyu Madaki
Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa zaman gidan yari zai ci gaba da gudana a lokaci guda kuma zai fara ne daga ranar da aka kama Hussaini.
Kamar yadda lauyan masu shigar da kara daga ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Barista Mahdi Aliyu Abdulrahman, ya gabatar da tuhumar.
Justice Watch News ta ruwaito cewa bayan sauraren shari’ar da kuma la’akari da shaidu da hujjojin da aka gabatar a gaban shari’ar, shugabar alkali, Mai shari’a Maryam Sabo, ta samu wanda ake tuhumar da laifin a karkashin sashe na 222 na kundin laifuffuka na penal Code, Laifin Kisan da ake tuhumarsa.
Kotun ta kuma yanke wa Kassim Hussain hukunci a karkashin sashe na 224 na kundin laifuffuka ba tare da yanki masa hukuncin kisa ba.
Sashe na 224 ya na nuni da cewa, Duk wanda ya aikata kisan kai ba tare da hukuncin kisa ba, za a yanke masa hukuncin daurin rai da rai, ko tara ko duka biyun.
