News
Jami’an KAROTA Sun Kama Kayan Da Aka Sace A Makarantar Gwamnati Na Fiye Da Naira Miliyan 80
Jami’an Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) sun dawo da kayan ICT masu aiki da hasken rana da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan Mata Aisha Shehu, dake Kuka a karamar hukumar Fagge na fiye da Naira miliyan 80.
Babbar malamin makarantar, Hajiya Rufa’atu Mahmud Baffa, ta bayyana cewa barayin sun kutsa cikin dakin ICT na makarantar, inda suka cire bangon rufi da kayan solar sannan suka dauki kwamfutoci da sauran na’urorin zamani. Sai dai, jami’an KAROTA da ke sintiri da daddare sun gano kayan a wani wuri, inda barayin suka tsorata suka tsere.
Daraktan Gudanarwa na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da kishin kasa, inda ya tabbatar da cewa duk kayan da aka sace an dawo da su gaba ɗaya, kuma an mika su ga makarantar. Ya ce duk da barayin sun tsere, an samu nasarar kare dukiyar makarantar.
Kabir ya jaddada bukatar kara inganta tsaro a makarantu, musamman wadanda ke cikin shirin AGILE da Bankin Duniya ke tallafawa, domin ci gaba da bunkasa bangaren ilimi a jihar Kano.
