Connect with us

News

Kotu Ta Tisa Ƙeyar Ma’aurata Zuwa Gidan Kaso Bisa Zargin Su Da Kuntatawa Ƴaƴan Su.

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Wata Kotun Majistare da ke Jimeta Yola dake jihar Adamawa a ranar Talata ta tura wasu ma’aurata Abubakar Yuguda da Fatima Abubakar zuwa gidan kaso bisa zargin su da kuntatawa ƴaƴan Uwargida.

Advertisement

Alkalin kotun Musa Adamu shi ne ya bayar da umarnin a tsare  wandanan mutane a gidan kaso har zuwa ranar 21 ga watan Oktoba.

MATASA: Duk Da Wannan Tsadar Rayuwa Da Kuke Sha Amma Kun  Kasa Fitowa Kuyi Bore — Tsohon Minista

Adamu ya ce an yanke ranar sake zaman ne saboda bin diddigin tare kuma da binciko shaidu don tabbatar da laifin ɗaya daga cikin waɗanda ake tuhuma kafin a dawo kan dayan abokin aikata laifin.

Advertisement

Kamfanin Dillancin Labaran Kasa NAN, ta ruwaito cewa wanda ake kara na farko ya amsa laifuka biyun da ake tuhumarsa da su su ne hada baki da kuma cin zarafin yara, yayin da dayan da ake tuhuma yake amsa laifin da ake tuhumar sa.

ASP Iliya Akawu,Ɗan sanda mai gabatar da kara ya roki kotun da ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Oktoba, domin samun damar ci gaba da gudanar da bincike don samar da kwararan shaidun da za su tabbatar da laifin wadanda ake tuhuma.

Advertisement

Lauyan waɗanda ake tuhuma Mohammed Umar, wanda bai yi musu akan neman a dage shari’ar, ya nemi alfarma da kotu ta bayar da belin wadanda yake karewa, yana mai cewa za su gabatar da shaidu masu karfi a zama na gaba da zai gudana.

Tun da farko dai, masu gabatar da kara sun ki amincewa da bukatar neman belin inda suka ce laifin ba abinda za a bada beli ba ne sakamakon wadanda aka Musgunawa na nan kwance a asibiti suna jinya raunikan da suka samu.

Advertisement

“Rundunar ‘yan sanda da ma’aikatan lafiya suna kokarin sa ido kan yadda ake kula da lafiyar yaran da abun ya faru da su.

“Wanda ake kara na farko ta amsa laifinta sai dai bayar da belin zai yi wahala duba da zasu iya sake aikata wannan laifi

Advertisement

“Aikata wannan laifi ya nuna cewa wadannan mutane ba su da tausayi yaran da ba nasu ba,” in ji shi.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa yaran sun sha wahala sosai.

Advertisement

Haka kuma rundunar ta shaida wa kotun cewa, an dauki matakin ne sakamakon faifan bidiyo da aka ga Abubakar yana dukan Hafsat, da igiya saboda kawai ta yi fitsari.

Rahoton ya cigaba da cewa iyayen tabbas sun gaza sauke nauyin hakkin da ya ke kan su,Duk da cewa yaran na tsohuwar matar Abubakar ne.

Advertisement

Aikata wannan laifin ya ci karo da sashe na 60 da 209 (2) na dokar penal code na Adamawa 2018.

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending