News
Farashin Magunguna Sunyi Tashin Gwauron Zabi A Kasar nan.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar kanfanoni masu harhada magunguna ta kasa ta ce an samu karuwar kudin maganguna a kasar nan da kaso 300 bisa 100.
A cewar kungiyar, Kalubalen canjin kudi da kuma tsadar kayan da ake amfani dasu wajen samar magani, sune manyan dalilan da suka haddasa tashin magunguna a kasar nan.
Babbar Magana:An manta abin tiyata da ya kai girman faranti a cikin wata mata
A hirarsa da manema Labarai,Shugaban kungiyar, Oluwatosin Jolayemi, Ya ce kanfanonin harhada magunguna na shan wahala wajen samun canjin kudin kasashen ketare.
Haka zalika shima tsohon shugaban kungiyar masu kimiyyar hada magani ta kasa, Lolu Ojo , Ya ce kayayyakin da ake amfani dasu wajen hada magani sune abunda ke haddasa tsadarsa.
Babbar Magana:An manta abin tiyata da ya kai girman faranti a cikin wata mata
Wani labarin kuma Hukumar kare haɗɗura ta Najeriya ta ce akalla mutum 12 ne suka mutu a wani mummuna haɗari ranar Lahadi a kan titin Obajana-Lokoja a jihar Kogi.
Jami’in wayar da kan al’umma ACM bisi Kazeem ya tabbatar da mutuwar mutane cikin wata sanarwa da ya fitar wadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya wallafa.
Kazeem ya kuma ce akwai mutum shida cikin motar da suka ji munanan raunuka.
Ya ƙara da cewa haɗarin ya rutsa da wata mota ne ƙirar Toyota Hiace mai lamba MKA515ZD da wata gingimari.
Ya ce duka mutane 18 da ke cikin motar hayar maza ne.
Ya kuma shawarci matuƙa da su riƙa kiyaye yanayin gudunsu wanda hakan zai taimaka wajen rage yawan haɗura.
Haka kuma Gwamnatin tarayya ta ce ana shirin yin garambawul ga shirin N-Power domin daukar karin masu amfana da kuma tabbatar da biyan alawus ba tare da bata lokaci ba.
Shirin na N-Power wani shiri ne da ke da nufin bunkasa fasahar matasa da bunkasa harkokin kasuwanci.
Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ministar ta ce za a sake kaddamar da shirin tare da sabon tsari da kumakudiri.
Ta ce ma’aikatar na shirin kafa cibiyoyin jin kai a fadin kananan hukumomi 774 a matsayin wani dogon buri na kawar da talauci a kasarnan.