News
Babbar Magana:An manta abin tiyata da ya kai girman faranti a cikin wata mata

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An bar wa wata mata wani abin tiyata “da ya kai girman farantin cin abinci” a cikinta a wani asibiti da ke birnin Auckland a New Zealand.
An cire abin tiyatar ne daga cikinta wata 18 bayan ta haihu.
Tun lokacin da aka yi mata tiyatar take fama da raɗaɗi, kuma ta yi ta zuwa wajen likitoci daban-daban domin gano mai yake damunta.
Tinubu Ya Tafi Kasar Indiya Yayin Da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zabensa A Gobe
Masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun ce asibitotcin gwamnati ba sa lura da marasa lafiya kamar yadda ya kamata.
Sai dai ma’aikatar lafiya da lura da masu buƙata ta musamman ta yi watsi da wannan lamari, kamar yadda ta bayyana cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
“Mutanen da suka yi wannan tiyatar ba za su iya faɗin yadda suka manta da wannan abu a cikinta ba, kuma ba su iya kai wa ga ganin abin ba lokacin da suka kammala tiyatar,” in ji nasarwar.
Tinubu Ya Tafi Kasar Indiya Yayin Da Kotu Zata Yanke Hukunci Kan Zabensa A Gobe
Wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta ce ana shirin yin garambawul ga shirin N-Power domin daukar karin masu amfana da kuma tabbatar da biyan alawus ba tare da bata lokaci ba.
Shirin na N-Power wani shiri ne da ke da nufin bunkasa fasahar matasa da bunkasa harkokin kasuwanci.
Ministar jin kai da kawar da fatara, Betta Edu ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ministar ta ce za a sake kaddamar da shirin tare da sabon tsari da kumakudiri.
Ta ce ma’aikatar na shirin kafa cibiyoyin jin kai a fadin kananan hukumomi 774 a matsayin wani dogon buri na kawar da talauci a kasarnan.