Connect with us

News

Tsadar Rayuwa Na Hana Marasa Lafiya Da Dama Zuwa Asibiti —Likitoci

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Kwararru a fannin lafiya sun koka cewa, marasa lafiya da dama basu zuwa asibiti sai cutar da su ke fama da ita ta ta’azzara saboda da matsanancin kuncin rayuwa.

Advertisement

Binciken da Muryar Amurka ta gudanar na nuni da cewa, duk da sanin hadarin da ke tattare da rashin zuwa asibiti kan lokaci, mutane da dama a Najeriya sun gwammace jinyar kansu a gida sabida da rashin kudin jinya, abinda kwararu su ka bayyana a matsayin wani lamari mai hatsarin gaske da ke sanadin rasa rayukan mutane da dama.

Farashin Buhun Gawayi Ya Kai Naira 10,000 A Kano

A wani lokaci baya, Ministan lafiya Dokta Muhammad Ali Pate ya nuna damuwa kan yadda tsadar kayan jinya kan kawo cikas wajen kula da bukatun kiwon lafiya a Najeriya, inda ya nuna bukatar samar da wasu kayan da su ka hada da magunguna daga cikin gida.

Advertisement

Hatta tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana illar da ya samu a sanadiyyar yi wa kai magani ba tare da zuwa asibiti ba wanda ya sa ya shawarci mutane su gujewa hakan.

Kwanannan gwamnatin Najeriya ta sanar da yiwa mata masu juna biyu da basu da galihu tiyatar haihuwa kyauta domin ceto rayukan iyaye mata da jariran da su ke dauke da su, ganin yadda ake asarar rayuka da dama saboda da rashin biyan kudin kula da su marasa lafiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending