News
Farashin Buhun Gawayi Ya Kai Naira 10,000 A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Mazauna Birnin Kano sun koka kan yadda sukace farashin gawayi ya sakeyin tashin gwauron zabi a wannan lokacin inda ya kai Naira 10,000
A halin yanzu farashin dauri daya ya tashi zuwa N300, da kuma 500 yayin da N200 da ake sayar da shi a makonnin uku
Kungiyar Dillalan Mai IPMAN Da Matatar Dangote, Sun Cimma Yarjejeniyar Cinikayyar Mai Kai Tsaye
Buhun gawayin ya tashi daga 8,300 ya koma Naira 10,000 zuwa 10,500 akan sarin kowanne buhun guda saboda yawan amfani da shi da kuma Matsalar wutar Lantarki da ake samu a wannan Lokacin Najeriya.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa an samu karuwar yadda mutane ke yin tururuwar amfani da gawayin a wurare daban-daban sakamakon tsadar farashin gas.
Wani mai sayar gawayi a unguwar Tudun Yola dake Kano, Malam Sani Umar ya ce cewa tsananin tsadar rayuwa ya sa mutane jinginar da tukwanen iskar gas ɗin su na girki sun rungumi girki da gawayi a wannan Lokacin.
Malam Umar Mai gawayi ya Kara alakanta tashin gawayin da matsalar rashin wutar lantarki da ake samu a Najeriya inda aka samu kirin Naira 2,500 a duk buhu a cikin sati Uku
Haka zalika Wani dan kasuwa dake kano ya ce iyalinsa na amfani da gawayi yanzu saboda yawansu ba zai iya jure siyar Gas ba a wannan lokaci da ake ciki.
