News
Shugaban Tinubu Ya Naɗa Olufemi Olatubosun A Matsayain Sabon Shugaban Sojin Kasar Nageriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo ƙasar.
Kafin naɗa shi a muƙamin mukaddashin sojan Kasa Oluyede shi ne kwamandan runduna ta 56 da ke aiki a Jaji a jihar Kaduna.
Tun a makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu, tana mai cewa Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne ya maye gurbinsa a matakin riƙon ƙwarya.
Daga baya hedikwatar tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce “babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa” a tsarin aikinta.
Manjo Janar Olufemi Olatubosun Yanada Shekaru 56 Kuma kafin nadashi a mukaddashin sojan Kasa na Nageriya ya rike mukamai da dama sannan Yanada Ya’ya uku da mata.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
