News
Ana tsaka da shari’a ƴansanda sun kutsa kotu, sun fitar da ɗan uwansu da ake zargi da fashi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an rundunar ‘yansanda ta jihar Yobe sun kai samame a babbar kotun majistare da ke Potiskum, inda suka dauke wasu abokan aikinsu guda biyu da ake tuhuma da laifin hadin baki da kuma fashi.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a ranar 29 ga watan Oktoba, wasu ‘yansanda dauke da makamai daga ofishin shiyyar Potiskum sun shiga kotun da karfi, inda suka tayar da hankalin ma’aikatan kotu, lauyoyi da wadanda ake shari’a har suka nemi tsira.
Hakkin Mutane Sama Da Miliyan 20 Ne A Kanka Ba Mutum Daya Kawai Ba —Kawu Sumaila Ga Gwamna Abba
Haka kuma, an rawaito cewa ‘yansandan dauke da makamai sun dauke mutanen biyu da kotun majistare Hadiza Gimba ta riga ta yanke musu hukunci.
Tun da farko dai, rundunar ‘yansanda ta ki gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu don su fuskanci shari’a, duk da cewa an daga shari’ar sau da dama tare da umarnin kotu.
A cikin wata wasika da aka aike wa babban sakataren kotun daukaka kara da ke Damaturu, babbar kotun majistare ta zargi ‘yan sanda da kin karbar sammaci da aka tura musu.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, Dungus Abdulkarim, ya shaida wa manema labarai cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.
A cewar Mista Abdulkarim, rundunar tana sane da lamarin kuma har yanzu suna kan bincike.
A halin yanzu, reshen kungiyar lauyoyi ta Najeriya, NBA, a jihar, ta yi Alla-wadai da wannan mataki, inda ta yi barazanar dakatar da halartar dukkan kotuna a jihar.
Kungiyar lauyoyin, a cikin kudurinta bayan wani taron gaggawa, ta bukaci a cire, a binciki, kuma a gurfanar da kwamandan ofishin shiyya na yankin Potiskum da dukkan ‘yan sandan da suka shiga kotun da makamai don kai wannan hari.