News
Jami’an Hukumar DSS Sun Kama Wani Mai Fafutukar Kare Dimokradiyya Zubair A. Zubair A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Take-It-Back Movement (TIB) ta bayyana damuwa kan kamun daya daga cikin shugabanninta a Jihar Kano, Zubair A. Zubair.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumuntarta, Kungiyar ta sanar da cewa jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama Zubair a safiyar Alhamis.
Jirgin Ruwa Dauke Da Mutane Sama Da 200 Ya Kife A Jihar Neja
Duk da cewa ba a bayyana dalilin kamun ba, An majiyoyi sun ce yana da alaka da wani rubutu da ya wallafa a Facebook wanda ke caccakar gwamnatin Shugaba Tinubu.
KANO TIMES ta ruwaito cewa Zubair, ya kasance yana fitowa fili yana sukar gwamnatin Tinubu, an ce an kama shi a Kano sannan aka tafi da shi Abuja.
Barrister Harun Magashi, lauyan Zubair, ya tabbatar da cewa an mayar da shi zuwa Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Najeriya da ke Abuja.
“An kama Zubair jiya a Kano. da farko, DSS ce ta rike shi, amma daga bisani sun mika shi ga ‘yan sanda a Abuja,” in ji Magashi.
Da aka tambaye shi dalilin kama Zubair, Magashi ya ce:
“Har yanzu ba mu tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa ba. Sai dai muna zaton hakan yana da alaka da rawar da ya taka a zanga-zangar End Bad Governance da kuma suka da yake yi kan gwamnatin Shugaba Tinubu”
Wani dan rajin kare hakkin dan Adam kuma abokin Zubair, Nura Muhammad, ya tabbatar da kamun.
“Zubair ya kasance jarumi wajen kare hakkin al’umma, kuma kullum yana caccakar manufofin gwamnatin Tinubu. Kama shi ba abin mamaki bane, amma hakan cin zarafi ne ga ‘yancin fadin albarkacin baki,” in ji Nura.
