News
Gwamnatin Kano Ta Dawowa Da Jami’ar Northwest Sunanta Na Asali
Gwamnatin jihar Kano Ta Dawowa Da Jami’ar Yusuf Maitama University sunanta na Asali Northwest University.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dr. Yusuf Kofamata ya wallafa a shafinsa na facebook.
Ya ce, a zaman majalisar zartarwar jihar kano na 21 da ya gudana karkashin jagorancin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, majalisar ta amince maidawa da jami’ar sunanta na asalai wato NORHTWEST UNIVERSITY, KANO.
Jami’an Hukumar DSS Sun Kama Wani Mai Fafutukar Kare Dimokradiyya Zubair A. Zubair A Kano
Kazalika majasar zartarwar ta amince a sanya sunan na Yusuf Maitama Sule a abuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari domin girmamawa ga mai sunan.
Kofarmata ya kuma bayyana cewa tuni aka bayar da umarnin tura waɗannan dokoki zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano domin zamar da su doka, ciki harda gyaran dokar shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
