Connect with us

News

ASUU Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) reshen jami’ar jihar Bauchi, Sa’adu Zungur Unviersity (SAZU), sun sanar da shiga yajin aiki a kan rashin tsarin biyan kudin fansho da rashin biyansu wasu hakkokinsu na alawus.

Har ila yau, kungiyar ta ASUU ta bayyana cewa babu wani tanadi mai kyau na yin aiki da aka samar ga ma’aikatan jami’ar.

Jami’an Hukumar DSS Sun Saki Dan Fafutukar Kare Dimokradiyya Zubair A. Zubair 

Shugaban kungiyar ASUU a SAZU, Kwamred Auwal Nuhu, shine ya sanar da tsunduma yajin aikin yayin wani taro da manema labarai da ya gudana ranar Juma’a a harabar jami’ar da ke Yuli.

 

Kwamred Auwal ya umarci mambobin kungiyar ASUU na SAZU da su shiga yajin aikin wanda ya fara daga misalin karfe 12:00 na ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba, 2024.

Advertisement

“Kungiya ta gamsu cewa akwai sakaci da nuna halin ko in kula daga bangaren shugabancin jami’a da kuma bangaren gwamnati wajen biyan bukatun mu,” a cewar Kwamred Auwal.

Sannan, ya kara da cewa dukkan wani yunkurin kungiyar ASUU na ganin cewa hukumomi sun duba wadannan bukatu domin a warware matsalolin ya ci tura.

“A saboda haka, uwar kungiya ta amince mana cewa za mu iya shiga gagarumin yajin aiki na sai baba-ta-gani,” kamar yadda Kwamred Auwal ya bayyana.

Ya bayyana yanayin aiki a SAZU a matsayin ‘marar dadi’ tare da dora laifin a kan shugabancin jami’ar wanda ya gaza shawo kan matsalar duk da kiraye-kiraye da kungiyar ASUU ta dade ta na yi domin su dauki mataki.

 

“Ba zai yiwu mu cigaba da aiki a karkashin irin wannan yanayin ba. An tagayyara mambobinmu ta hanyar barinsu babu wani tsaro ta fuskar kudin shiga bayan shafe gomman shekaru su na aiki a jami’ar.

Advertisement

 

“Wannan yajin aikin shine mataki na karshe da kungiyar mu ta dauka bayan mun shafe tsawon shekaru ana tattaunawa ba tare da daukan wani mataki ba”, a cewar shugaban na ASUU a SAZU.a

Kwamred Auwal ya bayyana cewa yajin aikin ba zai kare ba har sai an dauki matakan zahiri domin kawo karshen matsalolin da ke damunsu.

WikkiTimes  ta tattaro cewa yajin aikin zai kawo tsaiko a harkokin koyo da koyarwa sannan zai shafi alakar da ke tsakanin mahukunta da ma’aikatan jami’ar.

A duk lokacin da kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki, dalibai su kan shiga halin kunci da damuwa saboda tsayawar karatunsu wanda kuma kai tsaye ya shaficigaban rayuwarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending