Connect with us

News

NAFDAC Ta Gargaɗi Masu Burodi Kan Amfani Da Sakarin Wajen Yin Burodinsu

Published

on

NAFDAC ta gargaɗi masu burodi kan daina amfani da wasu sinadarai 2 wajen yin burodinsu

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci, NAFDAC, ta gargaɗi masu harkar sarrafa fulawa da su a faɗin ƙasar nan da su daina amfani da sinadarin zaƙi na sakarin (saccharin) da sinadarin buromet (bromate) mai sa fulawa ta tashi.

Advertisement

Darakta-janar ta hukumar, Mojisola Adeyeye, ce ta yi wannan gargadi a lokacin da take ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

Shalkwatar Tsaro  Ta Yi Martana Kan Rahoton Amnesty

Ta kuma ba da tabbacin cewa duk gidan biredin da aka samu da amfani da waɗannan sinadarai zai fuskanci hukunci kuma za su yi amfani da tsarin bindiddigi na kayan abinci da aka sarrafa wajen gano masu kunnen ƙashi.

Advertisement

“Mukan fita waje domin gane wa idanunmu, kuma yawanci mukan samu ƙorafi ne ga wasu al’umma.”

Mun rufe gidajen sarrafa fulawa da dama saboda amfani da sinadarin buromet wajen yin biredinsu”.

Advertisement

Ta ce idan suka gano ko wani ya ɗanɗana kuma ya shigar da rahoto to lallai za su tabbata sun sun rufe gidan biredin.

Hakazalika ta ce akwai gidajen ruwa da suka rufe saboda rashin samar da ruwa mai inganci ko marar kyau.

Advertisement

“Sashen Bindiddiginmu na da muhimmanci domin ta da shi ne muke tabbatar da cewa abin da aka kawo mana muka gwada ingancinsa, shi ne wanda ake sayarwa a kasuwa.”

“idan muka yi bincike mukan tabbatar da mun taho da samfuri domin gwadawa a ɗakin gwaje-gwajenmu inda mukan gani gaskiyar abin da ke ƙunshe a cikin wannan abin.”

Advertisement

Ta ce a wasu lokutan bayan mutane sun yi rajista sukan koma su fara canja tsarin yadda suke samar da abu.

“wannan ne abin da muke kira da bindiddigin kasuwa,” ta faɗa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending