Sports
Ƴan Wasan Real Madrid Shida Ne Daga Cikin Fitattu 11 Na FIFPRO Na 2024.
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Ƴan Wasan Real Madrid Shida Ne Daga Cikin Fitattu 11 A Ƙwallon Kafa A Duniya Na Fifpro Na 2024.
Cikinsu har da Kylian Mbappe, wanda ya koma Sifaniya a bana daga Paris St German, sai dai babu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah a cikinsu.
Jami’ar KWASU Tayi Rangwamen N100,000 Ga Dalibai Masu Bukata Ta Musamman
An zaɓo yan wasan ne bayan auna ƙwazon da suka yi daga 21 ga watan Agustan 2023 zuwa 14 ga watan Yunin 2024.
Haka kuma sai ɗan wasa ya taka rawar gani a manyan wasa sama da 30, kafin ya samu damar shiga cikin fitattun.
Manchester City tana da ƴan wasa huɗu daga ciki da suka haɗa da Erling Haaland da Kevin De Bruyne da Éderson da wanda ya lashe Ballon d’Or, Rodri.
Wannan shi ne karon farko da Messi baya cikin fitattu 11 a ƙwallon kafa a duniya tun bayan 2006.
Ƙyaftin ɗin Argentina mai taka leda a Inter Miami ya yi kaka 17 a jere yana shiga jerin fitattun ƴan wasa 11 na duniya.
Ronaldo ya shiga fitattun ƴan ƙwallo 11 sau 16, wanda bai samu shiga na 2023 ba, haka kuma ba Salah duk da rawar da yake takawa a tamaula da cin ƙwallaye.
Messi da Ronaldo sune da ke buga tamaula a wajen nahiyar Turai, inda ɗan Agentina ke wasa a Amurka, shi kuwa na Portugal a Saudi Arabi.
Fitattun ƴan wasan tamaula 11 na duniya na FIFPRO na 2024
Mai tsaron raga: Ederson.
Masu tsare baya: Carvajal, Rüdiger da kuma Van Dijk.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, De Bruyne da kuma Rodri.
Masu zura ƙwallaye: Mbappé, Vini Jr. da kuma Haaland.
