Connect with us

Sports

Kasar Saudiyya za ta karɓi bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2034 – FIFA

Published

on

Kasar Saudiyya za ta karɓi bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2034 – FIFA

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta sanar a hukumance cewa kasar Saudiyya ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2034.

A tsawon shekaru, Saudiyya na fuskantar suka saboda take hakkin dan Adam da take yi, da tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, da kuma rashin ‘yancin mata.

Advertisement

Zargin Rashawa : Kotu Ta Tura Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello Gidan Yari

Duk da wannan damuwar, ƙasar ta kasance tana ba da gudummawa sosai a wasanni da kuma ɗaukar nauyin wasanni daban-daban na duniya, ciki har da Formula 1, dambe, golf, da wasan tennis.

Gasar cin kofin duniya ta 2034 za ta kasance karo na farko da aka fadada gasar ta kungiyoyi 48 a kasa daya.

Advertisement

Bayan haka, FIFA ta sanar da cewa, gasar cin kofin duniya ta 2030 za ta kasance tare da Spain, da Portugal, da kuma Morocco.

Gasar ta 2030 za ta fito da wani tsari na musamman, inda kasashe shida a nahiyoyi uku za su karbi bakuncin gasar. Za a bude wasanni uku ne a kasashen Argentina, Paraguay, da Uruguay.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending